Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-20 15:37:50    
Birnin Zhongqing ya sami babban ci gaba tun bayan da aka mayar da shi a karkarshin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye

cri

A cikin shekarun nan 10 da suka wuce, matsakaiciyar jimlar kudi da birnin Zhongqing ya samu daga wajen samar da kayayyaki ta kan karu da kashi 10.2 cikin dari a ko wace shekara, matsakaicin yawan kudi da ko wane mazaunin birnin ya samu ya wuce dalar Amurka 1,500 a shekarar bara, wato ke nan ya ninka sau uku bisa na shekarar 1996 kafin an mayar da shi a karkashin shugbancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye, haka kuma yawan kudin shiga da ko wane manomi da ke zaune a karkarar birnin ma ya karu da ninki daya.

A lokacin da ake bunkasa harkokin tattalin arzikin birnin Zhongqing da zamantakewar jama'arsa, an kyautata manyan ayyukansa a zahiri. Malam Wu Daofan, wani jami'in hukumar unguwa mai suna Dadukou ta birnin Zhongqing ya bayyana cewa, "a cikin shekarun nan 10 da suka wuce, birninmu ya sami manyan sauye-sauye har ba a taba samun irinsa ba a da. Da ma manyan ayyukan birninmu sun yi baya-baya ainun, amma yanzu sun sami kyautatuwa kwarai. A da matsakacin yawan kudi da birninmu ya kan kashe a ko wace shekara ya kai kudin Sin Yuan biliyan 20 zuwa 30, amma yanzu ya karu zuwa biliyan 200 zuwa 300 a ko wace shekara."


1 2 3