Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-19 15:41:55    
Cigaban da lardin Henan ya samu (Babi biyu)

cri

Lardin Henan ya kuma samu babban cigaba wajen aikin gona.kayan abincin da aka noma a kowace shekara ya kai sama da Ton miliyan 40.A cikin shekaru da yawa da suka shige,lardin nan yana kan matsayi na uku wajen noman auduga,da abubuwa masu ba da man girki da 'ya'yan itatuwa da ganyayen taba da kuma nama da sauran kayan abinci na dabbobin gida.Lardin nan ya samar da isashen abinci ga mutanensa na kashi 7.5 bisa dari na yawan mutanen kasa da filayen noma kashi 1.7 bisa dari na fadin gonakan kasa baki daya har ya zama wani muhimmin sansanin samar da kayan abinci ga duk kasa da bayar da babban taimakon samun tabbacin abinci a kasar Sin.

Lardin Henan ya kuma gaggauta bunkasa masana'antu,ya inganta shirye-shiryensa na masana'antu har ma an sami cikakkun tsare tsare 39 na masana'antu domin bunkasa tattalin arziki.Aka samu wasu muhimman masana'antun na yin kayan abinci da barasa da kera injuna da na'urori da kayan electronics da kayayyakin gine gine da narke karfuna da hada magunguna da kwal da man fetur da gas da kuma taba.Karin kudin kayyyakin masana'antun a shekara ta 2005 ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 492.3,wato ya karu da kashi 18.7 bisa dari idan an kwatanta da shi da na shekara ta 2004.(Ali)


1 2 3