Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-19 15:41:55    
Cigaban da lardin Henan ya samu (Babi biyu)

cri

A cikin shekarun baya lardin Henan ya samu nasarori masu kyau wajen inganta shirye shiryen tattalin arziki na aikin gona,musamman wajen noman alkama mai nagarta da samun naman dabbobi masu kyau.A kowace shekara ana iya gyara kayan abinci na sama da Ton miliyan 27 da naman dabbobin gida Ton miliyan biyu da dubu dari tara da madara na Ton miliyan daya da dubu 450 a wannan lardin.wasu kayan abincin da aka shirya a lardin sun yi suna har sun samu kasuwanni masu karin yawa.Shimkafa da kankana da tafarnuwa da barkono da aka noma a wasu wuraren lardin sun yi suna a gida da waje har ma an sayar da su a kasashen ketare.

Lardin Henan ya gaggauta bunkasa dazuzzuka.fadin filayen da aka dasa kanana itatuwa a ciki ya dau kashi daya cikin kashi goma na duk kasa.fadin filayen da aka dasa itatuwa a lardin ya kai kadada miliyan biyu da dubu dari shida da bakwai,da filayen itatuwa masu saurin girma na kadada dubu 270 da filayen itatuwa na tattalin arziki na kadada dubu 585.


1 2 3