
Dadin dadawa kuma, akwai wasu shiyyoyin da kamfanin samar da fim suka yi amfani da su domin samar da fim a Zhengding, wadanda suka hada da fadar Rongguofu da titin Ningrongjie da sauran wuraren da aka samar da shahararrun fim na kasar Sin. A cikinsu kuma, fadar Rongguofu, wata fadar gargajiya ce da aka gina bisa tsarin gini na zamanin daular Qing wato tsakanin shekarar 1644 zuwa ta 1911, ta yi suna ne sosai a matsayin Hollywood na gabashin duniya. An taba samar da fim misalin 80 a nan.(Tasallah) 1 2 3
|