
Birnin Zhengding mai dogon tarihi yana mallakar kyawawan kayayyakin tarihi masu dimbin yawa. Yanzu akwai wuraren yawon shakatawa na tarihi guda 7 da gwamnatin kasar Sin ke kiyayewa a nan, sa'an nan kuma, akwai wasu 5 da hukumar lardin Hebei ke kare su yadda ya kamata.
A cikin gidan ibada na Longxing da aka gina a shekarar 581 zuwa ta 618, an kuma fadada shi a shekarar 960 zuwa ta 1279, ana ajiye mutum-mutmin tagulla mafi tsoho da tsayi a duk kasar Sin da kuma sauran mutum-mutumin addinin Buddha na gargajiya. Gidan ibadan nan wuri ne mai kyau wajen nazarin tsarin gini na gidajen ibada na addinin Buddha na kasar Sin na zamanin daular Song wato tsakanin shekarar 960 zuwa ta 1279.
1 2 3
|