
Tsohon birnin Zhengding da ke lardin Hebei a arewacin kasar Sin yana kara jawo hankulan masu yawon shakatawa na gida da na waje saboda kyawawan gidajen ibada da hasumiyoyi da kofofi da aka samu a nan. An mayar da birnin Zhengding 'dakin ajiye dukiyoyi' ne domin kyawawan gine-gine da Sinawa suka gina a zamanin da a wajen, haka kuma ya zama daya daga cikin tsofaffin birane da suka fi shahara a arewancin kasar Sin.
A daular zamanin Chunqiu na kasar Sin wato shekarar 770 zuwa 476 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., birnin Zhengding hedkwata ce ta daular Xianyu. Sa'an nan kuma, yau da shekaru misalin dubu 2 da suka wuce, birnin Zhengding ya taba zama daya daga cikin muhimman cibiyoyin siyasa da aikin soja a arewacin kasar Sin.
1 2 3
|