Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 15:29:53    
Babban tsaunin Lvshan da ke arewacin kasar Sin

cri

A bayan gidan ibada na Beizhen, ana iya ganin wani ginin da ya yi kama da babbar fada a kan wani katon dutse a koluluwar Wanghaifeng, shi ne hasumiyar sa ido kan abokan gaba ta gargajiya, wadda alama ce ta babban tsaunin Yiwulvshan. An ce, a lokacin da ake rana, in an tsaya a wuri mafi tsayi a kololuwar Wanghaifeng, sai ana iya hangen tekun Bohai.

A bangare na tsakiya na babban tsaunin Lvshan, itacen Pine suna girma sosai. A lokacin kaka, kwarran itacen Pine tare da jajayen ganyayen da ke rufe bababn tsaunin Yiwulvshan suna da matukar kyan gani, har mutane na ta tunawa da su. Madam Li Dongmei, wadda ke jagorancin masu yawon shakatawa ta ce,

'A cikin dukkanin itacen Pine a babban tsaunin Lvshan, tsawon shekarun mafi tsufa ya wuce dubu 1, mafi kankanta kuma tsawon shekarunsa ya kai daruruwa. Itacen Pina na girma cikin dogon lokaci, shi ya sa ko da yake a idanunmu, suna da kanana, amma a zahiri kuma, sun yi shekaru da yawa suna girma a nan.'

In wani ya yi kasa ta benayen dutse, sai ya isa wani wuri mai fadi, inda ya iya ganin wani babban icen Pine masu tsawon shekaru fiye da dubu 10. A kusa da hanya kuma, akwai wata karamar rumfa, a ciki an dasa wani allon dutse, mazaunin wurin malam Liu Jian ya gaya wa wakilinmu cewa,

'A can da akwai wani icen Pine daban a wannan wuri. Yana girma a tsaye sosai, mutane na ganin cewa, icen Pine alama ce ta mutum mai kirki, shi ya sa an gina wannan rumfa domin tunawa da wannan Pine, an kuma dasa wani allon dutse don nuna cewa, mutum mai kirki shi ne wanda ya yi magana gaba-gadi kuma da zuciya daya, ya kuma kulla dangantaka tare da saura ba tare da buya kome ba.'(Tasallah)


1 2 3