Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 15:29:53    
Babban tsaunin Lvshan da ke arewacin kasar Sin

cri

Babban tsaunin Yiwulvshan shi ne shiyyar kiyaye halittu ta matsayin gwamnatin Sin da kuma muhimmin wurin yawon shakatawa na kasar Sin, inda aka iya samun wurare masu ni'ima da kuma wuraren gargajiya masu dogon tarihi da ke da nasaba da al'adun mutane. Gidan ibada na Beizhen a gindin babban tsaunin an gina shi ne yau da shekaru fiye da dubu 1 da suka wuce, shi ne kuma gidan ibada mafi cikakke da aka adana shi yadda ya kamata a kasar Sin, wanda aka gina domin yin kaka-gida a babban tsauni.

Mr. Wu ya kara da cewa, saboda yankin arewa maso gashin kasar Sin mafari ne ga masarauta na zamanin daular Liao, wato yau da shekaru fiye da 800 da suka wuce, da kuma na zamanin daular Qing, wato yau da shekaru sama da 300 da suka wuce, shi ya sa an fi samun kayayyaki da wuraren gargajiya mafi yawa a babban tsaunin Yiwulvshan, in an kwatanta su da na sauran zamanin daular Sin. Ya ce,

'Ya zuwa yanzu dai ana adana wani dandalin sadaukarwa da aka gina a zamanin daular Liao domin girmamawa gulkin da ke mulkin sararin sama. Ban da wannan kuma, ana kiyaye wani wurin tarihi na wurin koyar da yara na zamanin daular Liao a yau. Sarakuna 5 na zamanin daular Qing sun taba zuwa babban tsaunin Yiwulvshan sau 12 daya bayan daya domin bayar da abubuwan sadaukarwa ga gunkin sararin sama da kuma yin ziyara, sun kuma samar da rubuce-rubuce da zane-zane da kuma rubutattun wakoki da yawa. Daga baya kuma, an yi zanen sarakunan a kan kananan alluna domin nuna musu girmamawa, har zuwa yanzu ana kiyaye wadannan kananan alluna.'


1 2 3