Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 15:29:53    
Babban tsaunin Lvshan da ke arewacin kasar Sin

cri

Watakila kun taba jin sunayen manyan tsaunuka 5 masu muhimmanci na kasar Sin, wadanda babban tsaunin Taishan ke da matsayin farko a ciki. A zahiri kuma, akwai sauran manyan tsaunuka 5 daban da suka shahara ne saboda dogon tarihi da kyan karkara. Yau ma za mu gabatar muku da wani bayanin kan wadannan tsaunuka 5, sunansa shi ne babban tsaunin Lvshan da ke arewacin kasar Sin.

Cikakken sunan babban tsaunin Lvshan shi ne babban tsaunin Yiwulvshan, yana kewayen birnin Beizhen na lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Tsawonsa ya kai misalin kilomita 45, fadinsa kuma ya kai misalin murabba'in kilomita 630, tsayin babbar kololuwarsa ya kai mita 900 daga leburin teku. A cikin dubban shekaru da suka wuce, sarakuna na dauloli daban daban na kasar Sin sun yi gidajen ibada da gidajen tunawa a wannan babban tsauni, mawallafa da yawa kuma sun kai ziyara a nan, a karshe dai babban tsaunin Lvshan ya sami sigar musamman, wato kyan karkara da wuraren yawon shakatawa da ke da nasaba da al'adun mutane. Darektan hukumar kula da wurin yawon shakatawa na babban tsaunin Yiwulvshan malam Wu Taiyong ya yi bayani kan asalin sunan wannan babban tsauni, ya ce,

'A gaskiya, an yi sunan wannan bababn tsauni bisa lafazin yaren kabilar Donghu, wadda ita ce wani rashen kabilar Mengu na kasar Sin, ma'anarsa a bakin 'yan kabilar Donghu ita ce tsauni mai girma, haka kuma a bakin 'yan kabilar Man ita ce koren babban tsauni.'


1 2 3