Batu na farko shi ne tsara cikkakken shiri na maido da shawarwari tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnati.A cikin wannan shiri za a tsara lokacin yin tattaunawa da wurin da kuma batutuwan da za a tattauna a ciki.Amma bambamcin dake tsakaninsu shi ne gwamnatin Sudan ta bayyana a fili cewa ba za ta sake shiga tattaunawa kan babin da aka tanadaa cikin yarjejeniyar Abuja ba,kungiyoyi masu adawa da gwamnati suka bukaci a gyaran fuska na yarjejeniyar nan sosai domin neman samun karin riba. Wani batu dabam mafi muhimmanci da za a tattauna a wannan taron shi ne tura rundunar soja ta hadin gwiwa ta MDD da kungiyar hada kan Afrika.
Gwamnatin Sudan da kwamitin sulhu na MDD sun daddale kwarya kwaryar yarjejeniya kan batun nan.wannan rundunar soja ta hadin gwiwa ta kiyaye zaman lafiya ta kunshe da mutane dubu 26,kungiyar hada kan Afrika za ta nada wani mutum da ya kula da wannan rundunar.Bisa labarin da aka bayar,an ce a shirye yake kwamitin sulhu na MDD zai zartas da wani kuduri na bayar da izni ga sojojin hadin gwiwa da su dauki matakan da suka wajaba bisa ainihin halin da suke ciki yayin da suke tabbatar da tsaro a wurin da aka jibge su.
A gun taron duniya kan batun Darfur da yake halarta a Tripoli a wannan rana,shugaban tawagar gwamnatin Sudan kuma ministan kasa mai kula da harkokin waje Al-sammani ya bayyana cewa gwamnatin Sudan ta hakake cewa ba za a iya warware matsalar Darfur da karfin soja ba sai ta hanyoyin lumana da bangarorin da abin ya shafa za su bi ne kawai za a iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin.Ya ce nan gaba kadan za a fara share fage ga tattaunawar tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnati.an sa ran a fara karo na farko na shawarwarin kafin watan Satumba.(Ali) 1 2 3
|