Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 21:36:29    
An bude taron kasa da kasa kan batun Darfur na kasar Sudan

cri
 

Manzon musannan na kungiyar hada kan Afrika Salim ya bayyana cewa tare da mallam Jan Eliasson ya sha zuwa kasar Sudan da kasashen dake da makwabta da ita domin yin mu'amala kan abin da ya shafa kafin watanni biyar da suka shige.Ya yi fatan taron nan zai sake shimfida hanyar tattaunawar zaman lafiya ga gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnati.Salim ya yi nuni da cewa arangama da aka yi ta yi a yankin Darfur ba ta iya kulla kome ba illa ta kara dagula zaman lafiya da kwanciyar hankali na wannan yanki,kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa na Sudan su shiga shawarwarin zaman lafiya domin samo makoma mai kyau a wannan yanki.Za a saurari ra'ayoyi da shawarwari na mazaunan yankin Darfur a cikin yunkurin siyasa kan batun Darfur da ake yi domin maido zaman lafiya.

Mr Ali Al-turaiki ya jadadda cewa an kira wannan taro ne a wani muhimmin lokacin da batun Darfur ke ciki,dukkan mahalartan taron suna fatan a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma cikakken yankin kasa a kasar Sudan.Al-turaiki ya yaba kokarin da gwamnatin Sudan take yi wajen warware rikicin Darfur ta hanyar lumana,a sa'I daya kuma ya nuna baki cikinsa kan wasu kungiyoyi masu adawa da gwamnati sabo da ba su sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Darfur ba..Ya yi fatan taron nan zai samu sakamako mai amfani wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a kasar Sudan baki daya. Muhimman batutuwa guda biyu za a tattauna a wannan taro.


1 2 3