Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 21:36:29    
An bude taron kasa da kasa kan batun Darfur na kasar Sudan

cri

A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani kan taron duniya game da batun Darfur na kasar Sudan da aka fara. A ran 15 ga wata a birnin Tripoli,babban birnin kasar Libya an kira taron duniya kan batun Darfur na kasar Sudan domin tsara shirin maido da tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da dukkan kungiyoyi masu adawa da gwamnati a yankin Darfur. Wannan ne karo na biyu da aka kira taron kasa da kasa kan batun Darfur a kasar Libya a wannan shekara da muke ciki.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar hada kan Afrika da kungiyar kasashen larabawa da tarayyar Turai da kuma kasashen dake da makwabta da kasar Sudan da kasashe biyar masu wakilcin dindindin na kwamitin sulhu na MDD da gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnati sun tura wakilansu zuwa taron nan na yini biyu. Manzon musamman na sakatare-janar na MDD Jan Eliasson da wakilin musamman na kungiyar hadin kan Afrika Salim da mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin Afrika na kwamitin kula da al'amuran harkokin waje da hadin kan duniya na kasar Libya Ali Al-turaiki sun halarci taron kuma kowanensu ya yi jawabi a gun taron.

Mr Jan Eliasson ya bayyana cewa taron nan zai sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa na kasar Sudan da su karfafa hadin kansu wajen sake maido da shawarwari da kuma tabbatar da rawar da MDD da kungiyar hada kan Afrika za su taka kan batun Darfur na Sudan ta yadda za a sa kasashe dake da makwabta da Sundan su kara taka rawa kan warware rikicin.Ya yi fatan taron zai samu sakamako mai amfani ciki har da tsara cikakken shirin warware matsalar Darfur da mayar da dukkan bangarorin da abin ya shafa na Sudan cikin shawarwari da fara shawarwari masu amfani cikin tsanaki har ya kai ga daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya.


1 2 3