Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 15:53:41    
Ruan Wenping, wani malami nakasasshe na kasar Sin

cri

Bayan haka kuma, Malam Ruan ya fara ba da darrusa ga dalibai da harshen kabilar Yao da Sinanci. Da farko ya karanta darrusa da Sinanci, daga baya kuma ya yi bayani kan ma'anar darrusan da harshen Yao. Yanzu kusan dukkan dalibai suna iya yin magana da Sinanci kamar yadda ya kamata. Luo Dongyan, wata 'yar makaranta ta bayyana cewa,

"Lokacin da na shiga makaranta, na iya harshen kabilar Yao kawai, Malam Ruan shi ne ya koya mini Sinanci sau da yawa, shi ya sa yanzu na riga na iya yin tilawa daga hadda da Sinanci."

Ta haka, Ruan Wenping ya haye wahaloli iri daban daban da kuma tafiyar da aikinsa na koyarwa. Ba kawai ya dora muhimmanci kan ilmin da dalibai suka samu ba, har ma yana mai da hankali sosai kan horar da su daga dukkan fannoni. Ya kafa kungiyoyin wake-wake da raye-raye da rubutu da zane-zane da wasan kwallon kwando da kuma wasan kwallon pingpang. Yanzu ba kawai dalibasa suna nuna gwaninsu wajen wake-wake da raye-raye ba, har ma su kan je sauran makarantu don nuna fasaha.

A cikin zuciyar Ruan Wenping, makaranta gidansa ne. Domin makaranta da kuma dalibai, ya yi iyakacin kokarinsa ba tare da nadama da yin gunaguni ba. Sabo da ya samu maki da kyau sosai wajen aikinsa, shi ya sa aka zabe shi a matsayin malami mafi nagarta har sau da yawa, haka kuma ya taba samun lambar yabo wajen bayar da gudummowa ta musamman a fannin aikin koyarwa. Ban da wannan kuma a shekara ta 2005, an zabe shi a matsayin abin koyi na cin gashin kai na nakasassu a jihar Guangxi ta kasar Sin.(Kande Gao)


1 2 3