Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 15:53:41    
Ruan Wenping, wani malami nakasasshe na kasar Sin

cri

Ruan Wenping, gurgu ne kuma wani malami ne na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Kuma a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, yana dukufa kan bunkasuwar sha'anin ilmi na yankunan da ke fama da talauci na kasar Sin. Kuma bisa kokarin da yake yi, dukkan yara da ke kauyen da yake ciki sun shiga makaranta.

Kauyen Nonghuai na birnin Baise da Ruan Wenping ke ciki wani kauye ne na kabilar Yao mai fama da talauci, inda ake iya samun makarantar firamare daya tak wadda ake kiranta Nian'en a ciki. A shekara ta 1995, an aika da shi zuwan kauyen don tafiyar da aikinsa. Lokacin da Mr. Ruan wanda ya sha wahala sosai sakamakon ciwon kafafunsa ya iso wannan karamin kauye, da kuma ganin abubuwan da ke gaban idonsa, ya yi bakin ciki kwarai da gaske. Kuma ya gaya mana cewa,

"A wancan lokaci, dakunan makaranta suna lalacewa sosai, ciyawa ta fito ta yi girma a filin wasa da kuma rufin dakuna, haka kuma an iya samun ramuka da yawa a kan daben azuzuwa. Amma lokacin da na ganin wadannan yara, na tsai da kudurin tafiyar da aikina a kauyen."


1 2 3