Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 15:53:41    
Ruan Wenping, wani malami nakasasshe na kasar Sin

cri

A wancan lokaci, wahala mafi tsanani da ke gaban Ruan Wenping ita ce wata al'ada maras kyau ta wannan kauye, wato mata ba su iya shiga makaranta ba a maimakon lalacewar yanayin makaranta, sabo da haka da kyar a kan lallashi yara wajen shiga makaranta. Ganin haka, Malam Ruan wanda kafafunsa suke da nakasa, kuma bai gane harshen kabilar Yao ba ya roki wani dan kauyen da ya nuna masa hanya, daga baya kuma ya je gidaje daya bayan daya domin lallashin iyaye wajen amincewa da yaransu da su shiga makaranta. Bayan wata fiye da guda, a karshe dai Malam Ruan ya ziyarci ko wane gida na kauyuka biyar, kuma sahihancin da ya nuna ya burge ko wane dan kauye. Wei Jiayuan, daya daga cikin 'yan kauye ya gaya wa wakilinmu cewa,

"Lalle na nuna masa bambanci a wancan lokaci, na taba ganin cewa, ko wani nakasasshe yana iya raya sha'aninsa a cikin yankin da ke kan duwatsu? Amma ya zo gidana sau da yawa domin lallashi na wajen aikawa da yarana zuwa makaranta, ganin haka na amincewa da yarana su shiga makaranta bisa ra'ayin jarrabawa."

Ta haka, a karshe dai iyaye sun amince da aika da yaransu zuwa makaranta don samun ilmin tilas da gwamnatin kasar Sin ta bayar. Ya zuwa yanzu, dukkan yaran da shekarunsu da haihuwa ya cancanci samun ilmi na wurin sun riga sun shiga makaranta.

Bayan da yara suka shiga makaranta, wata matsala daban ta fito, wato Malam Ruan bai gane harshen kabilar Yao ba, shi ya sa bai iya yin hira tare da dalibansa ba. Amma wannan ba wata matsala ce ga Malam Ruan ba, kuma ya gaya mana cewa,

"na koyi harshen kabilar Yao ta hanyoyin daban daban, alal misali, na mayar da dalibina a matsayin malamina wajen koyon harshen. Kuma bayan shekaru uku ko hudu, na iya harshen kabilar Yao."


1 2 3