Watakila a shekaru 10 da suka wuce, akwai mutanen da ke shakkar ko za a iya tafiyar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a Hongkong yadda ya kamata, to, yau bayan shekaru 10 sun wuce, mutanen da ke rike da irin wannan tunani sun canza. Ga shi a cikin shekaru 10 da suka wuce tun bayan da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka a kan aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", mazaunan Hongkong suna kasancewa a matsayin maigida na Hongkong, kuma suna da dimokuradiyya fiye da da. Bisa goyon bayan da gwamnatin kasar Sin da kuma babban yankin kasar suke bayarwa, Hongkong ta cimma nasarar fuskantar barazana da kalubale iri iri, ciki har da matsalar kudi ta Asiya, kuma ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na cibiyar kudi da ciniki da ta sufuri ta duniya. Ga shi kuma a Macao, yau da shekaru takwas da suka wuce bayan da Sin ta maido da mulkinta a wurin, Macao ta kara samun albarka da kuma kwanciyar hankali, zaman rayuwar jama'arta ma ya kara kyautatuwa. Duk wadannan sun shaida mana cewa, manufar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" ta samar da wata hanyar lumana mafi kyau a wajen daidaita matsalolin mulkin kan kasa da yankin kasa da kuma matsalar kasancewar bambancin tsarurrukan mulki a cikin kasa daya, ta kula da moriyar bangarori daban daban, ma iya cewa, ta samar da wani kyakkyawan misali a wajen daidaita batun Taiwan da kuma tabbatar da sulhu a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, har ma tana jawo hankulan kasa da kasa, tana iya zama wani abin koyi ta fuskar daidaita matsalolin da ke shafar yankin kasa da mulkin kai da tsarurruka da kabilu da kuma addinai na duk duniya baki daya.(Lubabatu) 1 2 3
|