Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Alhaji Umaru Yahaya, wanda ya zo daga birnin Gusau da ke jihar Zamfara, tarayyar Nijeriya. A cikin wata wasikar da ya turo mana a kwanan baya, ya ce, "sau da yawa na kan ji kun ce ana aiwatar da manufar 'kasa daya amma tsarin mulki biyu' a Hongkong, shin mene ainihin ma'anar manufar, ko za ku iya ba mu cikakken bayani. To, domin amsa tambayar, bari mu kawo muku bayani a kan manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" ta kasar Sin.
Ma'anar manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" ita ce, a jamhuriyar jama'ar Sin, ana gudanar da tsarin gurguzu a akasarin yankunan kasar, amma a Hongkong da Macao da kuma Taiwan, ana gudanar da tsarin "jarin hujja". Amma babban sharadi da aka gabatar wajen aiwatar da manufar shi ne dole ne a amince da kasancewar "kasa daya", wato jamhuriyar jama'ar Sin, a kiyaye dinkuwar kasar da kuma cikakken yankinta, kuma a amince da gudanar da tsarin gurguzu a akasarin yankunan kasar. Sa'an nan, bisa wannan sharadi ne, ana iya gudanar da tsarurrukan mulki guda biyu.
1 2 3
|