Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-04 15:55:30    
Manufar kasa daya amma tsarin mulki biyu ta Sin

cri

Manufar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" wani muhimmin kashi ne na tsarin gurguzu na kasar Sin, kuma marigayi Deng Xiaoping ne ya gabatar da wannan manufa bisa hakikanin halin da Sin ke ciki, don neman tabbatar da dinkuwar kasar cikin lumana, da kuma tabbatar da kwanciyar hankali da albarka a Hongkong da Macao da kuma Taiwan.

A cikin wani muhimmin jawabin da marigayi Deng Xiaoping ya yi a watan Yuni na shekarar 1984, ya ce, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan matsayinta wajen daidaita batun Hongkong. Sau da yawa mun ce, bayan da gwamnatin kasar Sin ta maido da mulkinta a Hongkong a shekarar 1997, ba za ta canza tsarin zaman al'umma da tattalin arziki da ake gudanarwa a Hongkong a halin yanzu ba, kuma ba za ta canza akasarin dokokin Hongkong ba, bayan haka, hanyar zaman rayuwar mazaunan Hongkong da matsayin Hongkong na tashar jiragen ruwa mai 'yanci da kuma cibiyar ciniki da kudi ta duniya duka ba za a canja su ba, Hongkong na iya ci gaba da bunkasa huldar tattalin arziki tare da sauran kasashe da kuma shiyyoyi. Ya kara da cewa, manufar da za mu aiwatar ita ce "kasa daya, amma tsarin mulki guda biyu", wato a jamhuriyar jama'ar Sin, za a gudanar da tsarin gurguzu a babban yankin kasar, wanda ke da yawan jama'a biliyan daya, a yayin da za a gudanar da tsarin jarin hujja a Hongkong da kuma Taiwan, kuma ba za mu canja manufar ba har cikin tsawon shekaru 50, kuma za mu cika alkawarinmu.


1 2 3