Ko da yake shi ba dan wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ba ne a da, ya kuma gamu da matsaloli da yawa a farkon lokacin da ya fara aikin malamin horas da wasanni, amma Lu Shanzhen ya sabunta tunaninsa, a karshe ya sami wata kyakkyawar hanya wajen horar da 'yan wasa.
Lu Shanzhen da 'yan wasansa sun yi abin tarihi, amma lokaci na wucewa, suna fuskantar sabon kalubale. A watan Satumba na wannan shekara, za a yi gasar fid da gwani ta wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta duniya a karo na 40 a birnin Stuttgart na kasar Jamus. Kungiyar mata ta kasar Sin ba ta taki sa'a ba a cikin kada kuri'a cikin kugiya-kungiya, haka kuma ita kanta ta gamu da matsaloli, malam Lu ya san wannan sosai.
Duk da haka, Lu da 'yan wasansa sun share fage sosai wajen daidaita wadannan kalubale. Ba kawai gasar da za a yi a Stuttgart ba, sun fi dora muhimmanci kan taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, yana alla-alla wajen shugabantar kungiyarsa domin samun lambobin zinariya a gun wannan muhimmiyar gasa a mahaifiyarmu kasar Sin, domin wannan ne buri na dukkan Sinawa.(Tasallah) 1 2 3
|