Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-04 15:53:27    
Lu Shanzhen, malamin horas da wasanni na kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta mata ta kasar Sin

cri

A gun gasar fid da gwani ta wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta duniya da aka yi a birnin Copenhagen, hedkwatar kasar Denmark a shekarar 2006, shahararren malamin horas da wasanni Lu Shanzhen na kasar Sin ya jagoranci 'yan mata na kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta kasar Sin, sun sami ci gaba mafi girma a cikin shekaru 53 da suka wuce, wato a karo ne farko ne sun zama zakara a cikin gasa ta tsakanin kungiya kungiya ta gasar fid da gwani ta duniya. A cikin shirinmu na yau, za mu kara fahimtarmu kan wannan malamin horas da wasanni na kasar Sin.

Yanzu kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta mata ta kasar Sin tana karawa da takwarorinta na kasashen duniya, tana cikin hali mafi kyau a tarihi. Amma a zahiri kuma, kafin shekarar 2006, ba ta sami babban ci gaba ba. Malam Lu Shanzhen ya jure wahalhalu da yawa, ya kuma fahimci halin da kungiyar mata ta kasar Sin take ciki sosai, ya yi nazari kan matsalar da kungiyar mata ta kasar Sin ta shiga shekaru da yawa tana fuskanta, ya ce,'A galibi dai, kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta mata ta kasar Sin ta yi shekaru da yawa tana dogara da kananan gasanni, ba ta mai da hankali kan gasa ta tsakanin kungiya kungiya ba. Ta yi ta samun maki mai kyau a cikin gasannin uneven bars da wasan taka-ka-fadi, amma ba ta sami ci gaba a cikin gasannin wasannin horse vault da floor exercises ba.'


1 2 3