Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-04 15:53:27    
Lu Shanzhen, malamin horas da wasanni na kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta mata ta kasar Sin

cri

Duk da haka, 'yar wasa Cheng Fei ta kasar Sin ta canza irin wannan hali. A gun gasar fid da gwani ta wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta duniya da aka yi a shekarar 2005, Cheng Fei ta zama 'yar wasa ta farko a kasar Sin da ta zama zakarar duniya a cikin gasar wasan horse vault. A gun irin wannan gasa da aka yi a shekarar 2006 da kuma gasar cin kofin duniya ta wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe da aka yi a wannan shekara, Cheng Fei ta ci gaba da samun maki mai kyau.

Dadin dadawa kuma, sauran 'yan wasan kasar Sin 'yan mata suna nuna gwanintarsu. Domin wadannan nagartattun 'yan wasa ne kungiyar kasar Sin ta kyautata ingancinta sosai. Yaya malam Lu ya horar da wadannan 'yan mata? Lu ya yi bayanin cewa,'Na fi son horar da 'yan wasa bisa halin da ko wanensu ke ciki. Har kullum ina nace ga samun moriya mafi girma tare da biyan diyya mafi kankanta. Ko kusa ban mai da hanakali kan lokacin horo ba, ban taba kidayar lokacin horo ba. Ko wace 'yar wasan da nake horar da su suna shan bamban da juna a fannin lokacin horo.'

Dabarar horar da 'yan wasa da Lu Shanzhen ke bi ta sami nasara, 'yan wasan sun sami maki mai kyau, Lu kuma ya zama mutumin da ya yi abin tarihin wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe na kasar Sin. Amma a ganin Lu shanzhen, ya sami irin wadannan nasarori ne domin taki sa'a. Lu Shanzhen ya yi shekaru 30 yana horar da 'yan wasa a cikin kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ta kasar Sin. Ya gaya mana cewa,'A zahiri kuma, ni ba dan wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ba ne, ni ne dan wasan Sports Acrobatics a da. In wani bai sami ci gaba a wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe ba, za a horar da shi a wasan Sports Acrobatics. A lokacin can, an wargaza kungiyarmu ta wasan Sports Acrobatics, sa'an nan kuma, an yi karancin malaman horas da wasanni a kungiyar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe, shi ya sa zan sami damar shiga wannan kungiya.'


1 2 3