Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-03 15:47:35    
Tabkin Shengjinhu wata aljanna ce ga tsuntsaye

cri

Me ya sa tsuntsaye iri-iri masu yawan haka su zo tabkin Shengjinhu a lokacin hunturu? Kwararrun wurin sun yi karin haske cewa, tabkin Shengjinhu wani muhimmin wuri ne mai damshi a duniya. Tsuntsaye suna iya zama a fadama ko tabkuna ko kuma koguna, inda zurfin ruwa bai kai mita 6 ba kawai. Akwai filayen ciyayi da rairayin bakin tabki mai fadi a tabkin Shengjinhu, inda aka sami kifaye da kananan jatan lande da saiwoyin ciyayi da kuma kayayyakin lambu na daji da yawa, shi ya sa tsuntsaye suna sa isasshen abinci, suna iya gudun iska mai karfi da ruwan sama saboda ciyayin reed suna girma sosai a nan. Dukkansu sun bai wa tsuntsayen da suke rayuwa a tabkin a lokacin hunturu abinci da yawa da kuma kyakkyawar wurin zama.

Tabkin Shengjinhu ya shahara ne a duniya domin kyakkyawan muhallin halitta da kuma albarkatun tsuntsaye mai albarka. A ko wane lokacin kallon tsuntsaye, manazarta da masu yawon shakatawa da yawa na gida da na waje sun zo wannan tabki don kallon tsuntsayen da suke kishi. Shugaba Cheng Yuanqi na hukumar kula da shiyyar kiyaya halitta ta tabkin Shengjinhu ya gaya mana cewa,

'Lokacin da malam Jim Harris da ke aiki a Asusun kula da dabbobi na duniya wato WWF ya zo nan domin bincike, ya yi mamaki sosai saboda ganin tsuntsaye masu yawan haka, da kuma ire-irensu masu albarkan haka. Musamman ma ya nuna babban yabo ga kyakkyawan muhallin tabkin Shengjinghu domin ya taba ganin tsuntsayen hooded crane fiye da 300 da kuma na Oriental White Storks fiye da 200 a wani karo. Ban da wannan kuma, kwararre mai ilmin tsuntsun Snipe Mark Bart na kasar Australia da masani mai ilmin tsuntsun swan goose malam Nick na kasar Rasha da wakilan kamfanonin dillancin labaru, kamar su wakilan kamfanin dillancin labaru na Yomiuri na kasar Japan da sauran kwararru da manema labaru daga kasashen waje.'(Tasallah)


1 2 3