Malam Zhang Ancai ya yi shekaru misalin 30 yana tukin kwale-kwale don daukar fasinjoji a tashar jirgin ruwa a tabkin Shengjinhu. Ya san tsuntsaye masu yin hijira iri daban daban da su kan yi rayuwa a lokacin hunturu wannan tabki sosai. Ya yi karin bayanin cewa,
'Na taba ganin dubban tsuntsaye suna tashi a sararin sama a kan tabkin. Tsuntsaye na iri daya suna tafiya tare, tsuntsayen da ba na iri daya ba ba su tafiya tare. Dinya na daji wato wild goose a Turance suna tafiya tare, haka kuma, tsuntsayen ruwa masu siffar balbela wato swan suna tafiya tare. Dinya na daji sun tashi suna jerawa kamar siffar 'v', a wani lokaci ma suna jerawa a layi. Tsuntsaye cygnet suna tafiya cikin kungiya-kungiya, sun kuma jere a layi. Ban da wannan kuma, kukansu na shan bambam da juna.'
Don gudun kawo wa tsuntsaye illa a zaman rayuwarsu ta yau da kullum, an kayyade masu yawon shakatawa da su kalli tsuntsayen a wuraren da ke nisa da inda tsuntsayen ke zama. Yana kasancewa da wasu tuddai a bakin tabkin Shengjinhu. A wani bangare na wadannan tuddai akwai ruwa, a wani bangare daban nasu kuma akwai kwarran ciyayi, shi ya sa wadannan tuddai wurare ne mafiya kyau wajen more idon mutane da kyan karkara da kuma kyawawan tsuntsaye. Saboda an kiyaye shiyyar kare halitta daga abubuwa masu gurbata muhalli, haka kuma ruwan tabkin na da tsabta, ya kan gangara sannu sannu, shi ya sa albarkatun halittun da ke zama a cikin ruwa ya yi yawa kwarai a cikin tabkin Shengjinhu, ta haka tsuntsaye da yawa sun zo nan a lokacin hunturu saboda sun iya samun isasshen abinci a tabkin.
Malam Yin Li ta yi shekara daya kawai tana aikin nazarin tsuntsaye a shiyyar kiyaye halitta ta tabkin Shengjinhu. A lokacin da take waiwayen abubuwan da suka auku a farkon lokacin da ta zo tabkin Shengjinhu, har yanzu dai ta ji farin ciki ainun. Ta ce,
'Na taba ganin tsuntsaye misalin dubu 50 a tabkin Shengjinhu. Na ji farin ciki kwarai da gaske a zuciyata a wancan karo kamar yadda na sha zuma.'
1 2 3
|