A lokacin kaka na ko wace shekara zuwa lokacin bazara na shekara ta gaba, tsuntsaye masu yin hijira dubu dubai sun je shiyyar kiyaye halitta ta tabkin Shengjinhu da ke lardin Anhui a tsakiyar kasar Sin a nan. A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku da wannan shiyyar kiyaye halitta ta tabkin Shengjinghu, wadda aka kira ta aljannar tsuntsaye.
Shiyyar kare halitta ta tabkin Shengjinhu na cikin gundumar Dongzhi ta lardin Anhui na kasar Sin, fadinta ya wuce misalin kadada dubu 30, ita ce shiyyar kiyaye halitta da gwamnatin Sin ta ware. Tabkin Shengjinhu na daya daga cikin muhimman wuraren da tsuntsaye masu yin hijira suke rayuwa a lokacin hunturu a kasar Sin. Yawan ire-iren tsuntsayen da suke rayuwa da hayayyafar 'ya'ya a nan a ko wane lokacin hunturu ya kai 170 ko fiye. Yawancin wadannan tsuntsaye masu yin hijira sun zo nan daga Siberia da kasashen Mongolia da Australia da sauran wurare masu nisa. Wasu tsuntsaye masu daraja da kasar Sin ke fi mai da hankali kan kiyaye su sun kan yi rayuwa a nan a lokacin hunturu.
1 2 3
|