Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:38:27    
CPU da ake kira Loongson na kasar Sin zai shiga kasuwannin kasa da kasa

cri

Li Guojie, shugaban cibiyar nazari kan fasahohin na'urar kwamfuta ta cibiyar ilmin kimiyya ta kasar Sin yana ganin cewa, nazari da sayar da CPU kirar Loongson 2E ya shaida cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin fasaha mafi muhimmanci da ke cikin sana'ar sadarwa, wanda zai taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar fasahar sadarwa ta Sin har ma ta duk duniya. Kuma ya kara da cewa,

"yanzu ana samar da yawancin na'urorin kwamfuta da kananan na'urorin kwamfuta ne domin biyan bukatun masu kashe kudi da yawa. sabo da haka tabbas ne mu samar da kuma yada na'urorin kwamfuta da suke cancanci mutane masu samun kudade kadan. Watakila CPU da ake kira Loongson zai canja tsarin kasuwar CPU ta duniya a nan gaba. CPU kirar Loongson zai bayar da muhimmiyar gudummuwa wajen shimfida samar da kayayykin sadarwa ba tare da kashe kudi da yawa ba."

Ta hanyar hadin gwiwa tare da kamfanin lantarki na ST Micro, CPU da ake kira Loongson da kasar Sin take da ikon mallakar ilminsa zai samu yaduwa sosai a duniya. Bisa yarjejeniyar da cibiyar na'urar kwamfuta ta cibiyar ilmin kimiyya ta kasar Sin da kamfanin lantarki na ST Micro suka daddale, kamfanin zai kula da ayyukan samar da CPU da ake kira Loongson, da kuma shigar da irin wannan CPU cikin kasuwannin duniya ta hanyar sayarwa. Ban da wannan kuma kamfanin zai biya kudin yin amfani da fasahar CPU da wasu kadaden da ya samu sabo da sayar da irin wannan CPU ga cibiyar nazari kan fasahar kwamfuta ta kasar Sin. Kuma wannan shi ne karo na farko da babban kamfanin kasashen waje ya biya kudade sabo da yin amfani da fasahar zane-zanen CPU na kasar Sin.(Kande Gao)


1 2 3