Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:38:27    
CPU da ake kira Loongson na kasar Sin zai shiga kasuwannin kasa da kasa

cri

Cibiyar nazari kan fasahohin na'urar kwamfuta ta cibiyar ilmin kimiyya ta kasar Sin ita ce ke kula da ayyukan nazari kan CPU da ake kira Loongson, kuma ta samu goyon baya sosai daga gwamnatin kasar Sin wajen kudaden nazari. A shekara ta 2005, cibiyar ta fara yin nazari kan CPU kirar Loongson 2E. Hu Weiwu wanda ya kula da wannan aiki ya gaya mana cewa,

"CPU kirar Loongson 2E ya kai matsayin zamani na duniya a fannin zane-zane. Kuma shi ne CPU na farko da ke da matukar inganci a duk duniya ban da CPU da kasashen Amurka da Japan suka kera. Saurin aikinsa ya kai sau biliyan hudu a ko wace dakika, amma yawan wutar lantarki da yake amfani da ita kalilan ce. Yanzu an riga an iya samar da irin wannan CPU da yawa."

Bugu da kari kuma yanzu wani kamfanin kasar Sin ya riga ya samar da na'urorin kwamfuta da ke da CPU kirar Loongson 2E, kuma ana yin gwajin sayar da shi a duk fadin kasar Sin. Farashin irin wannan kwamfuta ya kai kudin Sin Yuan 1599 kawai, kuma nauyin kwamfutar bai kai kilogram guda ba, wato ke nan ya kai kashi 10 cikin dari bisa na na'urorin kwamfuta na gargajiya, ban da wannan kuma yawan wutar lantarki da yake amfani da ita ya kai wajen kashi 20 cikin dari bisa na na'urorin kwamfuta na gargajiya. Hu Mingchang, mai kula da fasahar kwamfuta na kamfanin samar da irin wannan na'urar kwamfuta ya bayyana cewa,

"irin wannan na'urar kwamfuta tana da matukar kyau, ba kawai farashinsa yaba da rahusa ba, har ma ya iya biyan bukatun yau da kullum a fannin ayyuka da abubuwan ba da nishadi. Alal misali, ana iya yin amfani da wannan kwamfuta wajen aikawa da kuma samun wasikar E-mail, da sauraron wakoki, da kallon sinima da dai sauransu."


1 2 3