Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:38:27    
CPU da ake kira Loongson na kasar Sin zai shiga kasuwannin kasa da kasa

cri

Tare da bunkasuwar fasahohin sadarwa, kayayyakin sadarwa kamar na'urar kwamfuta da wayar salula da dai sauransu sun samu yaduwa sosai, kullum mutane su kan yi amfani da kayayyakin sadarwa iri daban daban yayin da suke aiki ko karatu ko kuma zaman rayuwarsu. Amma yawancin fasahohi masu muhimmanci na wadannan kayayykin sadarwa suna a hannun kasashe masu ci gaba, musamman ma CPU, injin kayayyakin sadarwa, kasashen Amurka da Japan da dai sauran kasashe kalilan ne suke iya kera su.

A shekara ta 2001, kasar Sin ta fara yin nazari da kuma kera CPU nata wanda ake kira Loongson. A shekara ta 2002, kasar Sin ta ci nasara wajen kera CPU kirar Loongson 1, ta haka an sa aya ga tarihin na'urorin kwamfuta na Sin wajen yin amfani da CPU na kasashen waje. Daga baya kuma kasar Sin ta fara yin nazari kan CPU kirar Loongson 2. Kuma ya zuwa yanzu an riga an fara samar da CPU masu yawa da ake kira Loogson 2E a kasar Sin, ban da wannan kuma ana hadin gwiwa tare da kamfanin lantarki na ST Micro da ya shahara sosai a duk duniya domin shigad da irin wannan CPU cikin kasuwannin duniya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan CPU kirar Loongson 2E da kasar Sin da yin nazari da kirkire-kirkire cikin cin gashin kai.


1 2 3