Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:28:22    
Gwamnatin Gordon Brown tana fuskantar jarrabawa

cri

Wani bayanin da aka buga cikin jaridar "the Sun" ta Britaniya ya yi nuni da cewa bankado shirin kai hare haren bama bamai da motoci a tsakiyar birnin London,nasarar ce da aka samu kwatsam.Bayanin ya ce wani dan giya ne ya kubutar da London daga hadari.Bayanin ya ce a ran 29 ga watan Yuni da sassafe da kimanin karfe daya,a cikin wani babban dakin nishadi dake kan titin Haymarket na birnin London,babban mai kula da dakin ya taimaki wani mutum da giya ta buge shi ya kira motar agaji don kai shi asiiti.Yayin da masu ceto sun isa wurin,sai sun gano hayaki na tashi daga wata motar Mercedes dake tsayawa a kan titi,nan take sun sanar da 'yan sanda.

Masu binciken al'amura suna masu ra'ayin cewa Brown ya kan tsaya daka kullum kan batun yaki da ta'addanci,a cikin kamfen neman zama shugaban jam'iyyar labour party da aka yi ba da dadewa ba,Gordon Brown ya jadadda cewa zai yi amfani duukan dabarun da zai iya dauka a fannonin soja da tsaro da lekon asiri da kuma tattalin arziki da al'adu domin yaki da 'yan ta'dda.Sabili da haka gwamnatin Brown ba ta iya sassauta matakin yaki da ta'addanci ba.Amma ta yaya Britaniya za ta kubutar da kanta daga barazanar 'yan ta'adda,wannan yana bukaar gwamnatin Brown ta nuna jan hali ta mayar da hankalinta kan manufar harkokin waje,ta rage katsalandan da aka yi ta yi tun daga zamanin Blair,ta kuma daidaita manufarta kan Iraq da Afghanistan.In ba haka ba tsatsaran matakan yin yaki da ta'addanci da ta dauka bai zai tsinana kome ba sai sha kashi kanta.(Ali)


1 2 3