Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:28:22    
Gwamnatin Gordon Brown tana fuskantar jarrabawa

cri

Har zuwa daren ranar daya ga watan Yuli,yan sandan musaman masu yaki da ta'addanci na Britaniya sun kame mutane biyar da ake tuhumarsu da hannu a ciki,daga cikinsu biyu an kama su ne a karkarar birnin Cheshire,dayan kuwa an kama shi a birnin Liverpool,ana tuhumarsu da hannu a cikin hare haren kai hari a brnin London da filin jirage na Glasgow.Sauran mutane biyu 'yan sandan sun kam su ne nan take daidai da yayin da suke tuka motar jeep mai cin wuta zunguri ginin.Ban da wannan kuma 'yan sandan sun kai samame a wasu gidajen da ke garuruwa na dab da filin jirage na Glasgow.sun kuma girke masu gadi a hanyoyin mota domin kare motocin da ake shakkarsu da bincike su.

Batutuwa guda uku da suka wakana cikin yan kwanaki bayan da Gordon Brown ya samu mukamin firayim ministan Britaniya,jarrabawa mai tsananni ga gwamnatin Brown kan ta yaya za ta tinkari wannan hali.A cikin jawaban da ya yi bi da bi cikin kwanaki biyu Mr Borwn ya bayyana ra'ayinsa da cewa na farko gwamnatinsa za ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta na kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.na biyu 'yan ta'adda ne masu alaka da kungiyar al-qaida su ne suka shirya hare haren da tabbatar da su,suna neman kai hari kan mabiya addinai daban daban da kawo assarar rayuka masu yawa.na uku Britaniya tana fuskanta barazanar harin ta'addanci mai tsananni .ya kamata jama'a su zama masu lura da kasance cikin shiri a ko yaushe.A ran 1 ga watan Yuli,sabuwar sakatariya mai kula da harkokin gida Miss Jacqui Smith ta kira taron kwamitin kula da rikici na majalisar gudanarwa a karo na hudu cikin kwanaki uku,ana sa ran cewa za ta sanar da 'yan majalisar dokoki a hukunce a ran biyu ga wata.

Bayan batun filin jirage na Glasgow,gwamnatin Britaniya ta karfafa matakan tsaro a filayen jiragen sama na London da Edinburg da Newcastle da Manchester da Birmingham da Blackpool da tasoshin jiragen kasa da kuma sauran filayen taruwar jama'a.Ban da wannan kuma an yi manyan taruruka da dama a birnin London a ran 1 ga watan Yuli,ciki har da babban taron kide kiden da mutane dubu dari shida ke hallarta domin tunawa da ranar cikon shekaru goma da rasuwar Diana a filin wasanni na Wembley da kuma budaddiyar gasar wasan raga na Wimbledon da kuma zanga zanga da 'yan luwaidi suka yi a cikin birnin,'yan sanda sun karfafa sentiri da matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da wadannan taruruka lami lafiya.

Duk da haka tsayayyen matakin da gwamnatin ta dauka da kuma gayyar kokarin da yan sanda suka yi,ba su iya hana kafofin yada labarai sun nuna shakku kan ayyukan yaki da 'yan ta'adda da gwamnatin ta yi ba.


1 2 3