Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 15:28:22    
Gwamnatin Gordon Brown tana fuskantar jarrabawa

cri

A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayanin da aka ruwaito mana kan gwamnatin Gordon Brown da take fuskanta jarrabawa bayan da hare haren da aka kai a kasar Britaniya.

A ran daya ga watan Yuli da yamma ne,aka gano wani kunshin da ake shakkarsa a gini mai lamba uku ma filin jiragen sama na Heathrow dake birnin London,nan da nan aka rufe ginin,daga baya kuma aka sake bude kofar ginin.Da ya ke har yanzu ba a san meme a cikin wannan kunshi ba amma an samu wannan batu ne bayan da aka gano yunkurin kai hare haren bama bamai da motoci biyu a tsakiyar birnin Londong a ran 29 ga watan Yuni wanda bai yi nasara ba da wata motar Cherokee da ta kama da wuta tana nufar babban girnin filin jiragen sama na Glasgow a ran 30 ga watan Yuni,Babu shakka hankalin sabuwar Gwamnatin Brown ya tashi.

Ya zuwa yanzu ana cigaba da bincike abubuwan dake cikin wannan kunshi da aka gano domin tabbatar da shirin kai hari na 'yan ta'adda ne.Duk da haka 'yan sanda sun tabbatar da harin da aka kai a filin jirage na Glasgow da shirin kai hare hare da aka shirya yi a tsakiyar birnin London wanda ya ci tura,hare haren ta'addanci ne.Bayan faruwar batun filin jirage na Glasgow,ma'aikatun tsaro na Britaniya sun tsananta matakan tsaro sosai.Wannan yana nufin cewa hare haren ta'addanci za su kusanto.


1 2 3