
Yanzu, 'yan makarantar sun yadada harkokinsu zuwa unguwannin birnin, inda suka rarraba takardun farfaganda da kananan katuna ga mazauna unguwannin. Bugu da kari, sun yi hadin gwiwa tare su wajen gudanar da gasar ka-cici-ka-cici a game da ilmin taron wasannin Olympic da kuma wasu gasannin motsa jiki. Ta wannan hanya ce 'yan makarantar suka yayata hasashen Olympic cikin zukatan mazauna birnin. Malama Zheng Liangqiong ta bayyana ra'ayinta, cewa wannan dai, wani irin ilmantarwa ne da ake yi a game da Olympic. Yaran sun samu damar zuwan unguwannin birni daga makaranta tare da zurfin ilmin da suke da shi dangane da taron wasannin Olympic. Hakan ya zama tamkar fassarawa ne ta babban take dake da cewa " Daukacin jama'a na halartar harkokin taron wasannin Olympic".( Sani Wang ) 1 2 3
|