Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 15:37:14    
Ilmantarwa a makarantun kasar Sin a game da Olympic

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da, cewa yunkurin gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic da dukkan al'ummomin kasa suke halarta ba ya rabuwa da yaduwar ilmi a fannin taron wasannin Olympic a cikin jama'a musamman ma yara matasa na kasa mai masaukin taron wasannin. Yanzu, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya rigaya ya nada makarantu 556 masu gwajin koyon ilmin Olympic a cikin yankin kasar Sin domin bada ilmi a wannan fanni ga yara matasa na kasar. To, yanzu sai ku biyo mu shiga daya daga cikin wadannan makarantu, inda za mu ga yadda ake ba da ilmi mai ban sha'awa a fannin wasannin Olympic.

Makarantar firamare ta Huajiadi tana a gabashin birnin Beijing, inda ya kasance da abubuwa iri biyu dake da sigar musamman, wato harkar " karamin kwamitin shirya taron wasannin Olympic" da harkar " yin farfaganda daga kowane aji a matsayin wata kasa zuwa unguwannin birni". " Karamin kwamitin shirya taron wasannin Olympic", yara 'yan makarantar su ne suka kafa shi bisa kwaikwayon hanyar kafa hukumomin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa da suka yi. Kowanen mamban karamin kwamitin, an zabe shi ne ta yakin neman zabe da kuma kada kuri'u da daukacin yara sama da 900 na makarantar suka yi. An yi shelar kafa wannan karamin kwamitin shirya taron wasannin Olympic ne a watan Oktoba na shekarar 2005, wanda ke kunshe da mambobi 74, wadanda aka zabe su ta hanyar daukar aiki bisa kwangila da kuma yin lacca a fili. Da zarar aka kafa karamin kwamitin, sai nan da nan aka kafa karamin gidan rediyo don watsa shirye-shiryen wasannin Olympic, da kebe filayen farfaganda kan wasannin Olympic da kuma kaddamar da mujallarsu a game da wannan fanni. Lallai dukann ayyukan da abin ya shafa na gudana lami-lafiya.


1 2 3