Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 15:37:14    
Ilmantarwa a makarantun kasar Sin a game da Olympic

cri

Wata 'yar makaranta mai suna Li Qimai dake da shekaru 10 da haihuwa, 'yan makarantar sun gabatar da ita don ta zama shugabar karamin kwamitin taron wasannin Olympic. Tana cike da imanin cewa, nauyin da karamin kwamitin ya rataya a wuyansa, shi ne kusantar da 'yan makaranta da taron wasannin Olympic na Beijing bisa kokari matuka da ake yi. Cewa ta yi, " Sannu! Ni ce Li Qimai, wato shugabar karamin kwamitin shirya taron wasannin Olympic. Babban nauyin dake bisa wuyana shi ne kula da harkar bada ilmi a fannin taron wasannin Olympic ga 'yan makarantarmu. Abin da muke iya yi domin taron wasannin, shi ne kusantar da 'yan makarantar da taron wasannin Olympic, ta yadda za su samu karin haske a game da wannan fanni.''

Harkar 'Yin farfaganda daga kowane aji a matsayin wata kasa zuwa unguwannin birni' ta taso ne bayan kafuwar 'karamin kwamitin shirya taron wasannin Olympic'. Kowanen ajin makarantar ya zabi kasashe 23 masu karfi na wasannin Olympic a matsayin wata kasar da yake wakilta. Makarantar firamare ta Huajiadi ta yi kwaikwayon salon da akan bi wajen gudanar da taron wasannin Olympic, wato ke nan ta shirya ' Karamin taron wasannin Olympic'. Azuzuwa 23 na makarantar, kungiyoyin wakilai 23 ne dake halartar gasar. A cikin yunkurin halartar gasar, 'yan makarantar ba ma kawai sun gane yadda akan gudanar da taron wasannin Olympic, har ma sun samu karin ilmi game da al'adun kasashen da suka yi kwaikwayonsu. Malama Zheng Liangqiong ta makarantar ta yi farin ciki da fadi, cewa " ta wannan hanya ce 'yan makarantar suka samu bayanai kan labarin kasa, da tarihi, da ilmantarwa, da al'adu, da tattalin arziki da kuma siyasa na wadannan kasashe".


1 2 3