Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 15:32:46    
Yankin tsakiyar kasar Sin ya zama sabon yanki ne da ke jawo hankulan 'yan kasuwa na kasashen waje sosai

cri
 

Kamfanin Metro na kasar Jamus yana daya daga cikin kamfanoni mafiya girma na sayar da kayayyaki a duniya. Malam Huang Zhongjie, babban manajan sashen kula da huldar jama'a na kamfanin ya bayyana cewa, a ganin manyan kamfanonin sayar da kayayyaki na kasa da kasa, kayayyaki da ake sayar a yankin tsakiyar kasar Sin suna da iganci da rahusa, don haka kamfanonin suna cin gajiyarsu wajen kara karfin takara a kasuwanni. Ya ci gaba da cewa, "larduna da ke a yankin tsakiyar kasar Sin kamar Henan da Hunan dukanninsu manyan lardunan aikin noma ne. A nan akwai amfanin gona mai armashi sosai kuma da kyau. A wannan gami, mun aika da ma'aikatanmu masu odar kayayyaki da yawa zuwa yankin don hadin kanmu da manoma kai tsaye a fannonin nama da 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da sauransu, ta yadda za mu bude wata hanyar gyara kayayyakin abinci tare."

A watan Afrilu na shekarar bara, a hukunce, gwamnatin kasar Sin ta fara mayar da ayyukan raya yankin tsakiyar kasar cikin sauri bisa matsayin manyan tsare-tsarenta. A gun bikin baje kolin nan, Malam Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, nan da shekaru sama da 10 masu zuwa, 'yan kasuwa na kasashen waje za su sami kyakkyawar dama da ba su taba samu ba a da a yankin tsakiyar kasar Sin.(Halilu)


1 2 3