Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 15:32:46    
Yankin tsakiyar kasar Sin ya zama sabon yanki ne da ke jawo hankulan 'yan kasuwa na kasashen waje sosai

cri

Malam Arifianto Sofiyanto, ma'aikacin sashen tattalin arziki na ofishin jakadaci na kasar Indonesiya a kasar Sin wanda ya halarci bikin baje kolin , a karo ne na farko da ya sa kafa a yankin tsakiyar kasar Sin. Ya yi mamaki da matsayin bunkasuwar birnin Zhengzhou. Ya bayyana cewa, "kafin zuwanmu, muna ganin cewa, ba a sami bunkasuwa da kyau a tsakiyar kasar Sin ba. Amma da zuwanmu birnin Zhengzhou na lardin Henan, mun gano cewa, ana samun bunkasuwa cikin sauri sosai."

Ko da yake Malam Norbert Claussen, magajin garin Schwerin na kasar Jamus ya sha zuwa birnin Zhengzhou, amma duk da haka saurin sauye-sauyen birnin ya shere shi sosai. Ya bayyana cewa, "wannan ne karo na uku da na sauka a birnin Zhengzhou, ana raya yankin tsakiyar kasar Sin cikin sauri, na yi mamaki da haka."

Lalle, yankin tsakiyar kasar Sin yana kan matsayi mai rinjaye a wasu fannoni idan an kwatanta shi da na sauran yankunan kasar. Yawan kudi da ake kashewa wajen daukar 'yan kwadago a yankin ya dauki kimanin kashi 60 cikin dari bisa na yankunan gabashin kasar, fadin filayensa da ake iya kafa masana'antu ya yi ninki 1.4 bisa na yankunan gabashin kasar. Sabo da haka 'yan kasuwa na kasashen waje da yawa sun fara mai da hankalinsu ga yankin nan.


1 2 3