
A kwanakin baya, a birnin Zhengzhou na lardin Henan da ke a tsakiyar kasar Sin, an shirya bikin baje koli na ayyukan zuba jari a tsakiyar kasar Sin a karo na biyu. Manyan kamfanoni sama da 300 da ke cikin manyan kamfanonin kasa da kasa kamar kamfanonin Microsof da Metro da Carrefour da sauransu sun halarci bikin baje kolin. Yanzu, yankin tsakiyar kasar Sin ya riga ya zama sabon yanki ne da ke jawo hankulan 'yan kasuwa na kasashen waje kwarai.
Yankin tsakiyar kasar Sin yana hade da larduna 6 da ake kira Shanxi da Anhui da Jiangxi da Henan da Hubei da kuma Hunan, duk duk fadinsa ya kai muraba'in kilomita miliyan 1 da dubu 28, yawan mutanensa kuma ya kai miliyan 360. Yankin nan yanki ne mai yawan albarkatun kasa sosai da mutane masu yawa, nan kuma muhimmiyar mahada ce ta hanyoyin zirga-zirga da ke hada yankun kasar Sin ta arewa da kudu da yamma da kuma gabas. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an sami ci gaba cikin sauri wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin nan na kasar Sin.
1 2 3
|