Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-21 15:53:45    
Babbar ganuwar kasar Sin

cri

Bisa abin da aka rubuta cikin tarihi,an ce da akwai daulolin sarakuna da gidajen sarauta fiye da 20 suka gina babbar ganuwa tun lokacin da kanana kasashe suke yaki da juna a shekaru aru aru.Daular Chu ta fi dadewa wajen gina ganuwa domin kare kansu daga harin makiyayyi ko kasashen gaba na arewa.Daga baya daulolin Qi da Yan da Wei da Zhao da Qing sun bi sawunta wajen gina tasu ganuwa.Bayan da daular Qing ta kafa hadaddiyar kasa wadda ta hada sauran kananan kasashe,Sarki na farko na daular Qing ya tura wani babban janarsa da ya kai hari kan mutanen Xiongnu dake arewan kasar,ya kuma hada ganuwa ta kanana kasashe,daga nan wata babbar ganuwa mai tsawon kilomita sama da dubu biyar ya shimfidu a arewancin kasar Sin daga wurin Lintao a yammanci zuwa wurin Liaodong na gabas.Wannan asali ne na babbar ganuwar kasar Sin,duk da haka ganuwar da muke gani a yau yawancin sassanta sun ginu ne a daular Ming.

Har wa yau dai da akwai burbudin ganuwar da ake iya gani a yau wadda aka gina a daular Qing.Sarki na farko na daular Qing ya tura mutane sama da dubu dari uku wajen gina ganuwa ya kago abin mai ban al'ajabi a tarihin gine gine na Bil Adam.Babbar Ganuwa da aka gina ta taka muhimmiyar rawa wajen hana mutanen Xiongnu ketare ganuwa da hari da kare cigaban tattalin arziki da al'adu a bangarorin dake kudu da ganuwar.Babban mallami na kasar Sin Sun Yatsen ya ce "da ya ke sarki na farko na daular Qing ya yi azaba,ya bayar da nasa babban taimako wajen gina babbar ganuwa.taimakonsa ya fi na mallami Dayu wanda yake yunkurin magance ambaliyar kogi yawa."

Ana ci gaba da gina babbar ganuwar a daular Han.Daga Sarki Wen zuwa Sarki Xuan,an gina wata doguwar ganuwa da ta fara daga garin Dawanrs a yammaci zuwa gabar arewa ta kogin Heilongjiang a gabas wadda tsawonta ya kai kusan kilomita dubu goma,rabin tsawon hanyar silik yana shinfidu dab da ganuwar,lalle ganuwa ce mafi tsawo a cikin tarihi.Har zuwa daular Ming ba a dakatad da gina babbar ganuwa ba duk domin kare mutanen kudu da ganuwa daga harin mutanen Dadan da na Waci.Daga sarki Hongwu zuwa sarki Wanli,an gina babbar ganuwa har sau 20,daga nan wata ganuwa mai tsawo kilomita dubu shida da dari uku da hamsin ta ginu wato ta taso daga wurin Jiayuguan na lardin Gansu a yammaci zuwa wurin Hushan a gabashin lardin Liao a gabashin kasa.

Bisa wani labarin da aka bayar,an ce tsawon babbar ganuwar Sin ya kai kilomita dubu shida dari bakwai bisa bayanan da aka nuna cikin wani agogo mai auna tsawon hanya na wani basine wanda ya yi doguwar tafiya kan babbr ganuwar Sin.

Babbar Ganuwar Sin tana da daraja sosai ga masu yawon bude ido kuma tana da ma'anar tarihi da al'adu.Bayan da aka gyara tare da hankali,sassan Shanhaiguan da Juyunguan da Badaling da Simatai da Mutinanyu da Jiayuguan na babbar ganuwar sun zama mashahuran wuraren yawon bude ido da na shakatawa na kasar Sin da na kasashen waje.Idan ka samu damar yin yawo kan babbar ganuwar Sin,sai ka hau ganuwan dake kan tsauni,ka tuna al'amuran da suka faru cikin tarihi,sai ka ce sojojin dake bisa dawaki suna yaki da juna da takobi a gabanka.Ga shi a yau an dauki babbar ganuar Sin a matsayin abubuwa masu ban al'ajabi guda bakwai a duniya kamar su husumiyar pyramid na kasar Massar da filin fada da dabbobi na birnin Rome da husumiya dake birnin Piza na kasar Italiya.Ganuwar nan ta shaida dadadden tarihin al'adu da hikimomin na al'umman kasar Sin,haka kuma ta bayyana cewa mutanen kasar Sin suna cin gadon abubuwan tarihinsu yadda ya kamata.(Ali)


1 2 3