Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-21 15:53:45    
Babbar ganuwar kasar Sin

cri

Babbar Ganuwar Kasar Sin,manyan ayyuka ne a cikin tarihin wayewar kai na Bil Adam.An fara gina ganuwa a dauloli dabandaban kafin shekaru sama da dubu biyu da suka shige.Bayan da daular Qing ta kafa hadaddiyar kasa,sai ta hada sashe sashe na ganuwar.A lokacin da daulolin Han da Ming ke mulki,an sake manyan ayyukan gina babbar ganuwa da ba a taba samu irinsu ba shi ya sa ake kira "babbar ganuwar Sin" ayyuka ne masu al'ajabi a duniya.

Babbar ganuwar Sin tana shinfidu a rewancin kasar Sin,wato ta taso daga bakin teku na Shanhaiguan zuwa wurin Jiayuguan dake yammancin kasa,tsawonta ya kai kilomita dubu shida da dari bakwai,ana kiran "ganuwa mai tsawon Li dubu goma",bisa maaunin tsawo na gargajiya na kasar Sin.

An yi ta gina babbar ganuwa cikin shekarun sama da biyu da suka shige.Bisa abin tarihin da aka rubuta, an ce da akwi dauloli na sarakuna da gidajen sarauta na gargajiya fiye da 20 suka gina ganuwa,wato daga daular Chu ta fara gina tata ganuwa a karni na bakwai kafin bayyanuwar Innabi Isa har zuwa daular Ming (daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644 AD).Tsawon ganuwar da aka gina a daulolin Qing da Han da Ming ganuwar kawai ya wuce kilomita dubu biyar,idan aka hada su gaba daya,tsawonsu ya wuce kilomita dubu hamsin.Idan an gina wata ganuwa daban mai tsawon mitoci biyar da mai fadi mita daya cikin yin amfani da tubalolin da aka aza wajen gina babbar ganuwar Sin,ganuwar nan za ta iya kewaye duniya sau daya har da rara.


1 2 3