Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-21 15:53:45    
Babbar ganuwar kasar Sin

cri

Yawancin sassan babbar ganuwar Sin mai tsawo kilomita dubu biyar suna shimfiu ne ba bisa karkara kawai ba suna cikin tsaunuka ko kuma suna kan tuddai mafi tsayi.Wasu sassan ganuwar sun zauna kan fuskar duwatsu kamar yadda suke a kwance.Wani sashinta na hawa sama,wani sashinta na gangarowa kasa,sai ka ce wani dodo mai ban mamaki da karfi na tafiya kan tsaunuka,saboda haka aka mai da babbar Ganuwar Sin wata alama dake wakiltar al'ummar kasar Sin.An bude daruruwan kofofi a babbar ganuwar da dubu duban dakunan tsinkaya da na ba da alamun gargadi da wuta a bisa ta.Shi ya sa ganuwar Sin ta kara kyaun gani a kan duwatsu da tuddai sai ka ce wani babban abin fasaha mai al'ajabi da ya dauka hankulan mutanen duniya yana tsaye a gabanka.

Yayin da ka yi yawon bude ido kan babbar ganuwar kasar Sin,sai ka sa kafa a wurin Badaling dake kusa da birnin Beijing,wuri ne mafi kyaun gani inda wani sashin ganuwar ya shinfidu a kan wani tsauni kamar yadda yake a kwance,wannan sashen ganuwar na da tauri kuma an kiyaye shi yadda ya kamata.An ce da tubalin duwatsu ne aka gina wannan sashen ganuwar.tsawon ganuwar a wannan sashe ya kai mita 8 da digo biyar,fadin gindin ganuwar ya kai mita 6 da digo biyar,fadin saman ganuwar ya kai mita 5 da digo bakwai.Dawaki hudu ko mutane goma na iya tafiya kafada da kafada bisan ganuwar.Wannan sashen ganuwar shi ma yana kan tsauni wani bangare yana sama wani bngare daban yana kasa wani kuma a karkace. Sashen Badaling yana goshin babbar ganuwar kasar Sin a wurin Juyunguan,da akwai tsaunuka masu tsawon mitoci dubu daga leberin teku a kudu da arewa da babbar ganuwar.Idan ka tsaya kan kolin babbar ganuwar,ka iya tsinkayi wurin mai nisa dake da tsauni daya bayan daya kamar gajimare ke tasowa maras iyaka.Da ka tsinkayi yammancin babbar ganuwar sai ka ga filayen ciyawa da bishiyoyi da kuma wata madatsar ruwa mai walkiya.Da ka tsinkayi kudancin ganuwar sai ka ga gine gine masu benaye da yawa na tsaye.a arewancin ganuwar hanyoyin mota suna kwanta cikin kwari.wuri ne mai kyaun gani.

Ban da wannan sashe da akwai sassa da dama da su cancanci a yi yawon bude ido a kai,kamar su sashen Jinshanling da sashen Mutianyu da sashen Simatai da sashen Gubeikou na babbar ganuwar.Sashen Huangyaguan dab da birnin Tianjin da sashen Shanhaiguan dake cikin lardin Hebei da sashen Jiayuguan dake cikin lardin Gansu,su ma shahararun wurare ne ga yawon bude ido kan babbar ganuwar kasar Sin.

Lokacin da aka kashe wajen gina babbar ganuwar kasar Sin ya fi tsawo a duniya,babbar ganuwa ta kasance manyan ayyukan tsaron kasa ne na soja a zamanin yaki da makamai,ta kuma kunshi gumi da hikimomi na kakani kakanin mutanen kasar Sin haka kuma alama ce da abin alfahari ne na al'ummar kasar Sin.


1 2 3