Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-21 12:54:48    
Bayan komowar Hongkong cikin kasar Sin cikin shekaru 10, tattalin arzikinta ya samu bunkasuwa lami lafiya

cri

Ban da kokarin da gwamnatin yankin musamman ta Hongkong ta yi da kanta, Mr. Henry Tang ya ce, abin da ya kawo ambatan musannan shi ne goyon bayan da Hongkong ta samu daga wajen gwamnatin tsakiya. Ya jiko sosai ya ce, "A lokacin da muke kokarin haye wahalolin da muka gamu da su wajen tattalin arziki, gwamnatin tsakiya da Hongkong sun daddale "shirin kara dankon zumunci tsakanin babban yankin kasar Sin da Hongkong" a tsakaninsu, bisa wannan shiri za mu iya himmantar da mutanen babban yankin kasa da su yi yawon shakatawa zuwa Hongkong, da gudanar da harkokin kasuwanni cikin 'yanci."

Mr. Henry Tang ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya ta nuna matukar goyon baya ga Hongkong, bunkasuwar da aka samu wajen tattalin arzikin Hongkong ba ta rasa nasaba da bunkasuwar tattalin arziki na babban yankin kasar Sin. Ya bayyana cewa, a lokacin da za a bunkasa Hongkong a nan gaba, ya kamata a yi la'akari da matsalar ba da taimako ga sha'anin bunkasa kasar Sin baki daya. Ya ce, "Nan gaba, ko za mu iya ci gaba da ba da taimako ga kasar mahaifarmu wajen sha'anin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje? Domin amsa wannan tambaya, ya kamata mu mai muhimmanci wajen bunkasa sha'anin hidima da na kudi a nan gaba."(Umaru)


1 2 3