Bisa matsayinta na babbar cibiyar Asiya da tekun Pasific a fannoni 3 wato kudi da ciniki da kuma zirga-zirgar jiragen ruwa, Hongkong kullum tana jawo hankulan mutane wajen bunkasa tattalin arziki tun bayan shekaru 10 da suka wuce da aka maido da ita karkashin mulkin kasar Sin. Yaya aka fuskanci kalubale cikin wadannan shekaru 10 wajen tattalin arzikin Hongkong? Yaya halin da ake ciki yanzu a wannan fanni? Kuma ina ne makomarta wajen bunkasa tattalin arziki? Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin, wakilinmu ya je neman labaru wajen Mr. Henry Tang Ying-yen, shugaban hukumar kudi ta yankin musamman na Hongkong. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan labari.
Mr. Henry Tang ya gaya wa wakilinmu cewa, bayan da aka maido da Hongkong karkashin mulkin kasar Sin a shekarar 1997, an samu matukar goyon baya daga gwamnatin tsakiya, mutanen Hongkong kuma sun yi kokari tare, ban da wannan kuma an samu kulawa da taimako daga wajen 'yanuwanmu da yawansu ya kai biliyan 1.3 na babban yankin kasar Sin, sakamakon haka Hongkong ta sake raya kanta cikin 'yan shekarun nan da suka wuce daga duk fannoni. Mr. Henry Tang ya ce, "Matsakaicin yawan tattalin arzikin da aka samu cikin shekaru 3 da suka wuce ya karu da kashi 7.6 bisa 100 a kowace shekara, wannan ba safai akan ga irin sa ba cikin tsarin tattalin arziki wanda ya riga ya samu bunkasuwa sosai."
1 2 3
|