Amma hanyar da aka bi cikin shekaru 10 da suka wuce a Hongkong ba na a zo a gani ba ne, wato an gamu da kalubale da yawa. Mr. Henry Tang ya ce, kalubale mafi girma da aka gamu da shi wajen tattalin arzikin Hongkong shi ne matsalar kudi ta Asiya. Fasahohin da Hongkong ta samu wajen kubutar da kanta daga mawuyacin hali su ne, daga wani fanni gwamnatin yankin musamman ta sauke nauyinta ga mutanen Hongkong da kuma ayyukan da gwamnati ta gudana, daga wani fanni daban kuma gwamnatin yankin musamman ta kaddamar da wani shirin kasafin kudi mai kyau bayan shawarar da ta yi da mutanen sassa daban-daban, sabo da haka an shimfida zama mai dorewa wajen kasuwannin kudi, da kyautata zaman rayuwar jama'a.
1 2 3
|