Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:13:39    
'Yan makarantar sakandare sun soma yin rawar waltz a kasar Sin

cri

Dadin dadawa, Tian yana ganin cewa, ana bukatar tunani a kan halin da ake ciki a kasar Sin a lokacin da ake yada rawar waltz da sauran rawa a tsakanin 'yan makarantun firamare da midil. Ya ce,'Ya kamata mu mai da hankali a kan yadda za a yada rawa a tsakanin dukkan 'yan makarantun firamare da midil. Kasarmu wata kasa ce mai girma, kuma mai yawan kabilu. Sa'an nan kuma, ya zama wajibi ne mu yi tunani kan halin da ake ciki a wasu wurare marasa ci gaba. Yaran da ke zama a wurin za su dauki lokaci domin karbar rawar waltz, shi ya sa nake ganin cewa, irin wannan tunani na da kyau sosai, amma za a bukaci daukar matakai sannu sannu wajen yada shi a duk kasar.'

Makarantar midil mai lambar 101 ta Beijing wata makaranatar midil ce mai inganci a Beijing. 'Yan makarantar da ke karatu a mataki na 2 na makarantar sakandare sun fara koyon rawar waltz tun daga ran 1 ga watan Satumba na wannan shekara. Malam Jiang Jiaqian, wanda ke aiki a nan ya bayyana cewa, 'yan makarantar ba su motsa jiki yadda ya kamata a da ba. Duk da haka in suna yin rawar waltz, mai yiwuwa ne irin wannan hali zai sami kyautatuwa. Ya ce'Mai yiwuwa ne 'yan makarantar za su nuna sha'awa kan rawar waltz domin ba su taba yinta a da ba, don haka za su yi allah-alla wajen koyonta.'

Malam Jiang ya yi hasashen cewa, a maimakon rashin sha'awar motsa jiki, saboda 'yan makarantun firamare da midil suna karatu tukuru a ko wace rana, ba su da isasshen lokacin motsa jiki. Yanzu mayar da yin rawa a tsakanin 'yan makarantun firamare da midil a matsayin dasarin tilas na tabbatar da bai wa 'yan makarantun firamare da midil isasshen lokaci a fannin motsa jiki. Saboda haka, Jiang ya yi imanin cewa, yada rawar waltz a cikin makarantun firamare da midil na sa kaimi kan ci gaban yara da matasa na kasar Sin daga dukkan fannoni.(Tasallah)


1 2 3