Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:13:39    
'Yan makarantar sakandare sun soma yin rawar waltz a kasar Sin

cri

Rawar waltz wata irin fasahar rawa ce da ake yi cikin natsuwa da kuma ban sha'awa, haka kuma wani muhimmin bangare ne na rawar wasannin motsa jiki. A 'yan kwanakin nan da suka wuce, irin wannan rawa ta jawo hankulan mutane sosai a kasar Sin, saboda ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta dauki wani sabon mataki a kwanan baya, ta mayar da rawar waltz a matsayin darasin tilas ga dukkan 'yan makarantar sakandare.

Yauzu ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta shirya ta kuma fito da tsari na farko na rawa a tsakanin 'yan makarantun firamare da midil na kasar Sin, ta tsai da kudurin yada shi a dukkan makarantun firamare da midil tun daga farkon sabon wa'adin karatu a ran 1 ga watan Satumba. Rawar waltz ta zama rawar tilas ga 'yan makarantar sakandare. A kwanan baya, shugaban sashen wasannin motsa jiki da kiwon lafiya da fasaha da ilmi na ma'aikatar ilmi ta kasar Sin malam Yang Guiren ya bayyana cewa, makasudin daukar wannan mataki shi ne domin ana fatan 'yan makaranta za su shiga harkokin fasaha da wasannin motsa jiki cikin himma da kwazo, za su fita wajen dakunan aji, za su je filayen wasa domin motsa jiki.


1 2 3