A halin yanzu dai, ingancin yara da matasa ya jawo hankulan rukunoni daban daban zamna al'ummar kasar Sin. Binciken da aka yi ya nuna cewa, a cikin shekaru 20 da suka wuce, karfin shaka ko fitar da numfashi a cikin huku da sauri da kuma karfi da sauran ma'aunai iri daban daban na ingancin jikin yara da matasa na kasar Sin yana ta raguwa, ban da wannan kuma yawan wadanda ke da kiba fiye da kima ya ninka sau daya bisa na yau da shekaru 5 da suka wuce. Ana ganin cewa, ban da tsarin abinci kuma, muhimman dalilan da suka haifar da wadannan batutuwa su ne domin 'yan makarantun firamare da midil suna fuskantar babbar matsin lamba a fannin karatu, sun kuma yi karancin lokacin wasannin motsa jiki. Yin rawa a tsakaninsu a cikin makarantu na matsayin gina hanyar zaman rayuwa, sa'an nan kuma, yana iya motsa jikunansu, shi ya sa sabon matakin nan da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta dauka ya sami babban yabo daga mutane da yawa.
Shehun malami Tian Yilin na kwalejin ilmi na jami'ar harkokin wasannin motsa jiki ta Beijing ya yi hasashen cewa, saboda zaman al'ummar kasar Sin yana ta samun ci gaba, musamman ma kasar Sin tana kara yin mu'amala da kasashen duniya, shi ya sa 'yan makarantar midil na kasar Sin suna bukatar motsa jiki ta hanyar zamani. A cikin wannan hali ne rawar waltz ta fito. Rawar waltz wata irin rawa ce ta zaman jama'a, wadda ke samun karbuwa a duniya a yanzu. Koyon irin wannan fasaha na ba da taimako wajen kyautata kwarewar yara da matasa na kasar Sin ta fuskar ilmin rayuwar jama'a da kuma gina siffofin jikunansu da kuma kyautata ingancinsu. Tian ya ce,'Saboda zaman rayuwa na yau da kullum da na al'adu na ta samun kyautatuwa, shi ya sa kamata ya yi mu sabunta hanyoyin ba da ilmi a makaranta. A ganina, yin rawar waltz a dukkan makarantun firamare da midil, musaman ma a makarantun sakandare, yana da muhimmanci sosai, haka kuma yana da ma'ana mai zurfi a tarihi.'
1 2 3
|