Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:12:07    
Wasannin Olympics na shekarar 2008

cri
 

A lokacin wasannin Olympics na Beijing, za a gudanar da wasanni iri iri, ciki har da manyan wasanni 28 da kuma kananan 302, kuma za a fara gudanar da wasannin daga ran 6 ga watan Agusta na shekarar 2008 har zuwa ran 24 ga watan, wato za a fara yin gasar wasan kwallon kafa kafin bikin bude wasan.

Game da sunan alamar da za ta alamanta gudanar da wasannin Olympics na Beijing, sunan shi ne "Dancing Beijing", ko kuma "Beijing mai annashuwa" da yaren Hausa. Alamar dai ta kasance wani hatimi na kasar Sin. A cikin hatimin, an yi amfani da fasahar harafin Sinanci, an mayar da rubutun sunan Beijing da ya zama tamkar wani mutumin da ke rawa. Bayan haka, a cikin alamar, an yi amfani da launin ja sosai, wato launi ne da Sinawa ke fi kauna, sabo da a ganin Sinawa, launin ja alama ce ta fatan alheri. Wannan alamar da za ta alamanta gudanar da wasannin Olympics ta bayyana irin tunani na mutanen gabashi da kuma al'ada ta daban mai inganci na wayewar kasar Sin. Sa'an nan, yana kuma bayyana kaunar zummar wasannin Olympics da al'ummar kasar Sin suke yi da kuma alkawarin da suka dauka wajen gudanar da wasannin.

Mun dai yi muku dan bayani a kan wasannin Olympics, amma kamar yadda malam Ibrahim Zubairu Othman ya tambaye mu, idan kuna son neman bayanai game da shirye-shiyen Olympics da za a yi a Beijing a shekarar 2008, kuna kuma iya yin amfani da wannan adireshin internet don karanta cikakkun bayanai, wato www.beijing2008.cn.(Lubabatu)


1 2 3