Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:12:07    
Wasannin Olympics na shekarar 2008

cri

A wannan mako, za mu amsa tambayoyin da shugaba Mohammed Idi Gargajiga daga Gombawa CRI Listeners Club da ke jihar Gombe, tarayyar Nijeriya ya yi mana. A cikin wasikar da ya turo mana, ya ce, ina nuna yabo da jinjinawa tare da godiya ga wadanda suke gabatar da wannan fili na amsoshin wasikunku, sabo da ganin yadda kuke nuna namijin kokari wajen binciko wa masu sauraro bayanai masu gamsarwa, wannan ya kara ba ni sha'awa kwarai da gaske, sabo da haka, ina so wannan fili ya amsa mini wadannan tambayoyi nawa tare da cikakken bayani. Ran nawa ga watan nawa zuwa ran nawa ga watan nawa, kuma a wane filin wasa ne za a yi bikin bude wasannin Olympics na Beijing na 2008 da kuma rufe shi? Kuma mene ne sunan da aka lakabawa alamar da za ta alamanta gudanar da wasannin Olympics na Beijing 2008? Kuma filayen wasanni nawa ne da za a yi amfani da su wajen gudanar da wasannin Olympics na Beijing? wasanni iri nawa ne za a yi a lokacin gudanar da gasar Olympics na Beijing? Ba ma shugaba Mohammed Idi Gargajiga kawai ba, hakika, masu sauraronmu da yawa su ma su kan yi mana tambayoyi dangane da wasannin Olympics da za a gudanar da shi a birnin Beijing. Misali, Ibrahim Zubairu Othman daga jihar Kaduna ya ce, shin idan mutum yana neman bayanai game da shirye-shiryen Olympics da za a yi a Beijing, wane adireshin internet ne za a yi amfani da shi? To, masu sauraro, domin amsa tambayoyin, bari mu kawo muku wasu bayanai dangane da wasannin Olympics da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008 mai zuwa.

Za a gudanar da bikin bude wasannin Olympics na karo na 29 a birnin Beijing a ran 8 ga watan Agusta na shekarar 2008, da misalin karfe 8 da dare, sa'an nan za a yi bikin rufe shi a ran 24 ga watan, kuma za a gudanar da su a babban filin wasa na kasar Sin, wanda ake kuma kiransa "shekar tsuntsu", sabo da irin siffarsa tamkar wata babbar shekar tsuntsu ce. Wannan babban filin wasa na kasar Sin ya kuma kasance filin wasa mafi muhimmanci a lokacin wasannin Olympics na shekarar 2008, ban da bikin bude wasan da kuma na rufe shi, za a kuma gudanar da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da kuma wasan kwallon kafa a nan filin. Filin ya fi burge jama'a ne da irin siffarsa ta musamman. Fadin filin ya kai muraba'in mita dubu 258, kuma yana iya daukar masu kallo da yawansu ya kai har dubu 91.


1 2 3