
Ban da wannan babban filin wasa na kasar Sin, akwai kuma sauran filayen wasa 30 da za a gudanar da wasanni iri iri a birnin Beijing, ciki har da sabbin filayen wasa 12 da aka gina su musamman domin wasannin Olympics na shekarar 2008, da filayen wasa 11 da aka gyara su ko kuma fadada su tare kuma da filayen wasa guda takwas na wucin gadi.
Bayan birnin Beijing, akwai kuma wasu filayen wasa a biranen Qingdao da Qinhuangdao da Shenyang da Tianjin da Shanghai da kuma Hongkong, wadanda za su hada kansu da birnin Beijing wajen gudanar da wasannin Olympics na karo na 29.
1 2 3
|