Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:24:58    
Kyakkyawan birni na Chongqing

cri

Kyan karkara da marmaron ruwa mai zafi da kuma abinci mai dadin ci muhimman alamu 3 ne na Chongqing a fannin yawon shakatawa. Akwai albarkatun marmaron ruwa mai zafi da yawa a nan da ba a taba ganin irinsa a sauran wuraren duniya ba. Yanzu hukumar Chongqing tana dora muhimmanci kan raya da kyautata marmaron ruwa mai zafi guda 5 don fadada girmansu da kyautata ingancinsui, tana neman raya kanta zuwa birnin marmaron ruwa mai zafi na duniya.

Yaya abincin Chongqing yake? Mutanen Chongqing sun fi son abinci mai yaji sosai, suna kuma son cin abinci mai zafi a cikin tukunyar da ke kan wuta. A ko ina na Chongqing, iska cike take da kamshi mai yaji. In ba ka saba da abinci mai yaji ba, to, masu dakunan cin abinci sun kyautata abincin da suke samarwa don biyan bukatarka.

A shekarun baya da suka wuce, Chongqing ta sami saurin bunkasuwar aikin yawon shakatawa. Shugaban hukumar yawon shakatwa ta Chongqing Wang Aizu ya nuna babbar aniya ga ci gaban aikin yawon shakatawa na Chongqing. Ya ce,

'Tunaninmu na raya aikin yawon shakatawa shi ne bunkasa Chongqing zuwa cibiyar rarraba masu yawon shakatawa a yammacin kasar da kuma cibiyar yawon shakatawa ta mafarin kogin Yangtze. A shekarar bara, yawan mutanen da suka kawowa birninmu ziyara ya kai misalin miliyan 68. Kudin da muka samu daga wajen aikin yawon shakatawa ya kai misalin kudin Sin yuan biliyan 36.4, yawansa ya kai kashi 9.8 cikin kashi dari bisa jimlar GDP ta birninmu. Mun mayar da raya aikin yawon shakatwa zuwa ginshiki na birninmu har zuwa shekarar 2010 a matsayin muhimmin aiki na bunkasa tattalin arzikin Chongqing.'(Tasallah)


1 2 3