Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:24:58    
Kyakkyawan birni na Chongqing

cri

Shirinmu na musamman na 'birnin Chong Qing a yau', wanda muka shirya ne domin murnar cikon shekaru 10 da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta fara shugabantar Chongqing kai tsaye. In an tabo magana kan shahararrun wuraren yawon shakatawa na kasar Sin, mai yiwuwa ne ka taba jin sunayen manyan kwazazzabai 3 na kogin Yangtze wato Sanxia na kogin Yangtze da kuma mutum-mutumin da aka sassaka na Dazu, a gaskiya kuma wadannan wuraren yawon shakatawa suna cikin birnin Chongqing, wanda birni ne mafi sabuntaka da ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye. Saboda akwai kyawawan wurare masu ni'ima da wuraren yawon shakatawa ta fuskar al'adun mutane da yawa, Chongqing tana kara jawo hankulan mutane da yawa daga wurare daban daban na duniya domin kawo mata ziyara.

Babu tantama kai ziyara ga Sanxia na kogin Yangtze ya fi jawo hankulan mutane a Chongqing. Sanxia kyawawan kwazazzabai ne da ke cikin kogin Yangtze, wanda ya fi girma a kasar Sin. Sanxia ta fi nuna kyan ganin wannan kogi mai tsawon kilomita 6300 ko fiye.

Sa'an nan kuma Sanxia na kogin Yangtze kwazazzabai ne mafiya girma a duniya da mutane suke iya yin yawo cikin jiragen ruwa a duk hanyarsu, suna iya more idanunsu da wurare masu ni'ima da kuma wuraren yawon shakatawa na halittu da na al'adun mutane da ke gabobin kogin. Ban da wannan kuma suna iya sauka bakin kogin domin yawon shakatawa. Malam Li, dan lardin Shandong, ya kai wa Sanxia na kogin Yangtze ziyara cikin jirgin ruwa. Ya ce,


1 2 3